(ABNA24.com) Yau Talata, 10 ga watan Muharam, milyoyin al'ummar musulmin Shi’a na gudanar da juyayi tare da alhinin tunawa da zagayowar ranar Ashura, ta tunawa da ranar da aka aiwatar da kisan gilla kan jikan fiyayyen halitta Manzon Allah (SAW) cewa da Imam Husaini (A.S) a cikin shekara ta 61 bayan hijira manzo.
A nan Jamhuriya musulinci ta Iran ana gudanar taruka na juyayin wannan ranar a sassa daban daban na kasar, a yayin da wasu kasashe irinsu Najeriya ake gudanar da jerin gwano.
A kasar Iraki miliyoyin musulmi ne musamman mabiya shi’a daga sassa daban daban na duniya ke tururruwa zuwa hubbaren Imam Husaini da ke birnin Karbala domin gudanar da juyayin wannan rana ta Ashura.
Rahotanni daga Iraki na cewa an karfafa kwararen matakan tsaro da nufin kare lafiyar masu juyayin. .
/129
10 Satumba 2019 - 12:40
News ID: 974552

Yau Talata, 10 ga watan Muharam, milyoyin al'ummar musulmin Shi’a na gudanar da juyayi tare da alhinin tunawa da zagayowar ranar Ashura, ta tunawa da ranar da aka aiwatar da kisan gilla kan jikan fiyayyen halitta Manzon Allah (SAW) cewa da Imam Husaini (A.S) a cikin shekara ta 61 bayan hijira manzo.